Dalglish ya bar mukaminsa na kocin Liverpool

Kenny Dalglish Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dalglish ya bar Liverpool

Kenny Dalglish ya bar mukaminsa na kociyan Liverpool.

Dan shekara 61 ,Dalglish, ya rasa mukamin nasa ne bayan wata ganawa da ya yi ta keke -da- keke da manyan masu kungiyar, John W Henry da Tom Werner a Boston.

Duk da cewa ta sami nasarar cin kofin Carling, ta kuma buga wasan karshe na cin kofin kalubale na FA, Liverpool, ta kammala gasar Premier a matsayi na takwas inda ta yi rashin nasara a yawan wasannin da tayi kusan dai dai da wadanda ta ci.

Dalglish din daman ya sake dawo wa kungiyar ne a karo na biyu bayan da Roy Hodgson, ya barta a watan Janairu na 2011, da farko a matsayin kocin rikon kwarya har zuwa karshen kakar wasannin.

Bayan kokarin da ya yi a karshen kakar wasannin aka tabbatar da shi a matsayin cikakken kocin kungiyar ranar 12 ga watan Mayu na tsawon kwantiragin shekaru uku, sai dai ya gaza cigaba da irin tagomashin da ya faro da shi kafin a tabbatar ma sa da mukamin.

Karin bayani