An bayyana tawagar 'yan wasan Ingila

'Yan wasan Ingila Hakkin mallakar hoto a
Image caption Wasu daga cikin 'yan wasan Ingila

Kocin tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Ingila, Roy Hodgson, ya bayyana jerin sunayen 'yan wasa ashirin da uku da kuma wadansu guda biyar 'yan zaman ko- ta-kwana wadanda ya zaba don su bugawa kasar Gasar cin Kofin Kasashen Turai, Euro 2012.

Sai dai daga cikin jerin 'yan wasan wadanda Steven Gerrad na Liverpool zai yiwa kyaftin, babu dan wasan Manchester United Rio Ferdinand.

Amma kamar yadda aka yi tsammani, akwai Wayne Rooney, wanda ba zai buga wasanni biyu na farko na Ingilan ba a Rukunin D, wanda za ta yi da Faransa ranar 11 ga watan Yuni da da kuma wanda za ta yi kwanaki hudu bayan nan da Sweden.

Daga cikin 'yan wasan dai, masu tsaron gida sune: Joe Hart, da Robert Green, da John Ruddy.

'Yan wasn baya kuma su ne Leighton Baines, da Gary Cahill, da Ashley Cole, da Glen Johnson, da Phil Jones, da Joleon Lescott, da kuma John Terry.

Sai 'yan wasan tsakiya: Gareth Barry, da Stewart Downing, da Steven Gerrard, da Frank Lampard, da James Milner, da Alex Oxlade-Chamberlain, da Scott Parker, da Theo Walcott, da kuma Ashley Young.

'Yan wasan gaba kuma sun hada da Andy Carroll, da Jermain Defoe, da Wayne Rooney, da kuma Danny Welbeck.

Sai kuma wadanda za su yi zaman jiran ko-ta-kwana: Jack Butland, da Phil Jagielka, da Jordan Henderson, da Adam Johnson, da kuma Daniel Sturridge.

Karin bayani