Ferdinand ba zai bugawa Ingila Euro 2012 ba

Rio Ferdinand Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rio Ferdinand ba zai shiga tawagar Ingila a Gasar Euro 2012 ba

Kocin Ingila, Roy Hodgson, ya kudiri aniyar tsallake Rio Ferdinand yayin bayyana sunayen 'yan wasan da za su bugawa tawagar kwallon kafar kasar a Gasar kasashen Turai ta bana, wato Euro 2012.

Shi kuwa Kyle Walker ba zai samu bugawa ba ne saboda raunin da ya yi.

Tun bayan kunnen dokin da tawagar 'yan wasan na Ingila ta yi da Switzerland a watan Yunin bara, lokacin da suka tashi biyu da biyu, Ferdinand, mai shekaru talatin da uku da haihuwa, bai sake bugawa tawagar kasar ba.

Idan an jima da rana ne dai za a bayyana sunayen 'yan wasa ashirin da ukun da suka samu shiga cikin tawagar.

Rahotanni na nuna cewa za a saka dan wasan tsaron bayan Chelsea John Terry, wanda aka sauke daga kan matsayin kyaftin a karo na biyu a watan Fabrairu, a cikin tawagar.

Ferdinand, wanda tsohon kyaftin din tawagar ne, ya sha fama da ciwon baya a 'yan shekarun nan, amma dai ya buga wasannin Gasar Premierhar talatin a kakar bana—tun kakar wasanni ta shekarar 2007 zuwa 2008 bai buga wasanni masu yawa haka ba.

Karin bayani