Leicester ta sayi 'yan wasan Manchester Utd

Ritchie De Laet Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ritchie De Laet

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta sayi Ritchie De Laet da Matthew James daga Manchester United; ko wannensu ya sa hannu a kan kwantiragin shekaru uku.

Ba a dai bayyana kudin da za a baiwa 'yan wasan biyu ba, wadanda kocin Leicester City, Nigel Pearson, ya kira "'yan wasa matasa biyu masu yunwar nasara".

Ba da jimawa ba ne dai United ta bayar da aron De Laet, wanda mai tsaron baya ne na tawagar kasar Belgium, ga Norwich City; ya kuma bugawa United din wasanni shida lokacin da yake Old Trafford.

Shi kuwa James, wanda dan wasan tsakiya ne na Ingila a tawagar 'yan kasa da shekaru 20, sau biyu ana bayar da aronsa ga Preston.

A cewar Pearson, "Ritchie da Matthew 'yan wasa ne da muka jima muna sa ido a kansu, kuma muna farin ciki da samun damar kawo su kungiyarmu.

"Babu shakka za su kara inganta kwazon 'yan wasanmu".