Bazan baiwa Sir Alex hakuri ba —Tevez

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto SKY SPORTS NEWS
Image caption Ba zan baiwa Alex hakuri ba

Dan wasan Manchester City, Carlos Tevez, ya ce ba zai nemi gafara daga kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ba akan daga wani kwali da yayi da aka rubuta ''Allah Ya jikan kocin'' a lokacin da 'yan city din ke breden murnar lashe gasar premier a titunan birnin Manchester.

Tevez ya ce abu ya zama kamar Ferguson shi ne shugaban kasar Ingila , idan ya fadi wani abu maras kyau akan wani dan wasa ba wanda yake cewa ya nemi gafara, amma da zarar wani ya yi wani barkwanci a kansa sai ace sai ya nemi gafara. Ni bazan bada wani hakuri ba, inji Tevez din.

Da yake zargin Ferguson din da faden abubuwa marassa dadin ji akan sa a baya ,Tevez ya kara da cewa babu wata alaka tsakaninsa da Sir Alex din.

Wani magoyin bayin kungiyar Manchester City din ne ya mikawa Tevez kwalin da ke dauke da rubutun a lokacin da suke kewaya birnin , kuma ana ganin martani ne akan amsar da Sir Alex ya bayar a 2009 da aka tambaye shi ko yana ganin akwai lokacinda United za ta zama kurar baya akan City, inda kocin ya ce ba dai a lokacin rayuwarsa ba.

Tun a baya dai kungiyar ta Manchester City, ta bada hakuri akan lamarin.

Karin bayani