Chelsea ta lashe gasar Champions League

'yan wasan Chelsea suna murna Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea ta lashe gasar Champions League a karon farko

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila ta lashe gasar cin kofin zakarun turai ta kwallon kafa wato Champions League.

Kungiyar ta lashe gasar ne bayan ta doke Bayern Munich a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda aka tashi 4-3.

Wasan wanda aka buga a filin wasan Bayern Munich da farko an yi kunnen doki ne bayan mintuna casa'in.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ke lashe gasar cin kofin zakarun turai.

Dan wasan Chelsea Didier Drogba ne ya jefa kwallon karshe a raga wadda ta baiwa Chelsea nasara.

Karin bayani