Sharapova ta lashe gasar Italian Open crown .

Maria Sharapova Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sharapova ta lashe kofin Italian Open Crown

Maria Sharapova ta lashe gasar tennis ta Italian Open crown a birnin Rome.

Maria 'yar kasar Rasha ta sami nasarar ce a kan Li Na 'yar kasar China a wasan da akayi kare jini biri jini tsakanin 'yan wasan biyu.

Kafin zubin karawar wasn ta karshe sai da aka dakata da wasan tsawon sama da sa'oi biyu saboda ruwan sama da ake yi a lokacin, kuma Li Na na kan hanyarta ta samun nasara, amma dawowa fagen wasan ke da wuya sai Sharapova ta sami galaba a kan Li din.

Da wannan nasara da Maria Sharapovan ta samu kofi na 26 ke nan ta dauka da fara wasan ta na kwallon tennis

Karin bayani