Mourinho ya sabunta kwantiraginsa da Madrid

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Jose Mourinho ya taka rawar gani sosai a Real Madrid

Jose Mourinho ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Real Madrid ta shekaru hudu wacce za ta zaunar da shi a kulob din har zuwa 2016.

Kocin na kasar Portugal, mai shekaru 49, ya zo Real ne a shekara ta 2010 inda ya lashe gasar Copa del Rey a shekararsa ta farko.

Ya kuma jagoranci Real Madrid zuwa lashe gasar La Liga ta farko a bana cikin shekaru hudu.

Mourinho ya kuma lashe gasar Premier ta Ingila sau biyu tare da Chelsea - sannan kuma ya lashe gasar League ta Portugal tare da Porto da kuma Serie A ta Italiya da Inter Milan.

Karin bayani