Utaka ya lashe gasar Lig 1 da Montpellier

John Utaka
Image caption John Utaka ya koma Faransa ne a watan Janairun bara daga Ingila

Dan wasan Najeriya John Utaka ya taimakawa kulob din Montpellier lashe gasar Ligue 1 ta kasar Faransa bayan da ya zira kwallaye biyu a wasansu na karshe.

Montpellier ta doke Auxerre ne da ci 2-1, abinda ya bata damar lashe gasar a madadin Paris St Germain da tazarar maki uku.

An shafe lokuta ana tsayar da wasan sakamakon fushin da magoya bayan Auxerre suka rinka nuna wa.

Sai dai Utaka da abokan kwallonsa sun nuna dattaku, inda suka dage sannan suka kafa tarihi.

John Utaka mai shekaru 30 da haihuwa ya koma Montpellier a watan Janairun 2011 daga kungiyar Portsmouth ta Ingila.

Wannan ne karo na uku a jere da Montpellier, ke taka leda a babbar gasar Faransa bayan sun shafe shekaru biyar a rukunin Ligue 2.

Burinsu dai a karon farko shi ne su kare matsayinsu.

Amma a yanzu sun kare kakar wasa ta bana a matsayin zakarun Ligue 1 a karon farko a tarihi.