Gasar 2014 na ke hankoro - Bent

Darren Bent
Image caption Darren Bent yana taka rawar gani a Aston Villa

Dan wasan Aston Villa Darren Bent ya ce kocin Ingila Roy Hodgson ya bashi tabbacin cewa zai shiga cikin shirinsa na wasannin share fagen shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2014.

Bent, mai shekaru 28, baya cikin tawagar Ingila ta gasar cin kofin kasashen Turai na Euro 2012, bayan da rashin lafiya ta ci karfinsa.

Sai dai Bent ya ce: "Hodgson ya shaida min cewa zan shiga cikin tawagar wasannin share fagen gasar cin kofin duniya.

"Fata na yanzu shi ne na taka rawar gani a Aston Villa a kakar wasanni mai zuwa, wanda daga nan zan samu damar shiga tawagar Ingila."

Bent ya samu rauni tun a watan Fabreru a wasansu da Wigan, kuma tun daga nan bai sake taka leda a gasar Premier ba.

Wannan ne karo na uku da Bent ke kasa halartar gasa ta duniya, ganin cewa bai samu halartar gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 da kuma 2010 ba.