Ministan Kamaru zai gana da 'yan wasan kasar

Ministan Kamaru zai gana da 'yan wasan kasar
Image caption Yan wasan Kamaru sun koka da rashin biyansu kudade

Ministan wasannin kasar Kamaru ya ce yana shirin ganawa da manyan 'yan wasan kwallon kasar kafin wasannin share fagen da za su yi a watan Yuni.

A baya an shirya ganawar ne a ranar 8 ga watan Mayu amma sai aka dage.

Gwamnatin na son shawo kan korafin da 'yan wasan ke da shi na kudade, wanda ya kaisu ga yajin aiki bara.

Hakan ne kuma ya sa aka dakatar da kyaftin din kungiyar Samuel Eto'o da Enoh Eyong.

Har yanzu dai babu Eto'o a cikin tawagar ta Kamaru, sai dai an sake gayyatar Eyong kuma zai halarci tattaunawar da za a yi da ministan.

"Za kuma su tattauna hanyoyin da za a bi wajen inganta yanayin aiki da kuma nasarorin da 'yan wasan za su iya samu.

Karin bayani