Ronaldo ya koka kan Rio Ferdinand

Rio Ferdinand Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi ta cece-kuce a kan matakin cire Rio Ferdinand

Cristiano Ronaldo ya nuna damuwa kan rashin saka Rio Ferdinand a jerin tawagar 'yan wasan Ingila da za su fafata a gasar cin kofin kasashen Turai ta 2012.

Ronaldo ya bayyana Ferdinand da cewa yana daya daga cikin 'yan wasan da suka fi kwarewa a duniya.

An ta yin cece-kuce kafin Roy Hodgson ya bayyana tawagar Ingila, inda aka mayar da hankali kan ko daya daga cikin John Terry ko Ferdinand zai samu shiga.

Dalili kuwa shi ne zargin da ake yi wa Terry da yin kalaman wariyar launin fata ga Anton Ferdinand, wanda kani ne ga Rio Ferdinand.

Sai dai kocin na Ingila Hodgson, ya zabi Terry kan Ferdinand, matakin da kuma ya gamu da maban-bantan ra'ayi.

Amma Ronaldo ya nuna damuwa kan yadda aka ajiye tsohon abokin wasansa a Manchester United, amma ya ce kocin ne ke da ikon yanke hukunci.