Ba ruwana da dawowar Chambers - Bolt

Usain Bolt Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Usain Bolt ne zakaran Olympic da duniya baki daya a tseren mita 100

Shahararren dan tseren kasar Jamaica Usain Bolt, ya ce bashi da wata damuwa game da fafatawa da Dwain Chambers a tseren mita 100.

'Yan wasan biyu za su fafata da juna a London 2012, bayan da Chambers ya samu damar shiga gasar sakamakon sauya dokar da ta dakatar da shi kan amfani da kwayoyin da aka haramta.

"Doka tana sama da komai," kamar yadda zakaran Olympic da kuma duniya Bolt ya shaida wa BBC Radio 5 live.

Idan doka ta ce babu matsala zai iya shiga a fafata da shi, to ni wanene da zan yi korafi. Akwai dalilan da suke sanya wa a yanke hukunci."

Dan wasan mai shekaru 25 ya kara da cewa: "Ni ina mayar da hankali ne kawai kan duk wanda zan yi wasa tare da shi kuma zan yi iya kokari naga na samu nasara."