Martinez na tattaunawa da Liverpool

Roberto Martinez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Roberto Martinez ya haskaka sosai bana a Wigan

Shugaban kulob din Wigan Dave Whelan ya ce kocin kulob din Roberto Martinez yana ganawa da Liverpool a birnin Miami na Amurka domin kasance wa sabon kocinsu.

Whelan ya baiwa Martinez izinin ganawa da Liverpool a makon da ya gabata, sannan kuma ya bashi wa'adin 5 ga watan Juni domin ya fayyace makomarsa.

"Roberto yana Miami, kuma ka san babu abinda zai kaishi face tattaunawa da masu kulob din Liverpool," kamar yadda Whelan ya shaida wa BBC.

"Yana da gaskiya kuma baya nuku-nuku, domin haka ina fatan ji daga gare shi nan da kwanaki biyu."

Tattaunawar ta Martinez ta bude fagen yunkurin da Liverpool suke yi na daukar sabon koci bayan da suka kori Kenny Dalglish a ranar 16 ga wata Mayu.

Karin bayani