Najeriya ta sha kashi a hannun Peru

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Super Eagles za ta kara da Namibia da Malawi a watan Yuni

Najeriya ta sha kashi a hannun Peru da ci 1-0 a ci gaba da shirye-shiryen da take yi domin tunkarar wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2014.

Masu masaukin baki sun lashe wasan sada zumuntar da aka buga a Lima babban birnin kasar ta Peru, ta hannun Paolo Guerrero a minti na 36.

Kalu Uche ya kai harin da ya daki turke a zagayen farko, sai dai Peru ne suka mamaye wasan tun daga nan.

Najeriya za ta kara da Namibia da kuma Malawi a watan Juni a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya.

A wani wasan sada zumuntar da aka buga a daren ranar Laraba, Botswana ta doke Lesotho da ci 3-0 a gida.

Karin bayani