Ivory Coast to kori kochinta ta nada sabo

Sabri Lamouchi
Image caption Sabon Kochin Ivory Coast

Kasa da mako daya kafin a fara wasannin neman shiga gasar cin Kofin

Duniya na kwallon kafa ta 2014, Ivory Coast ta kori kocinta Francois Zahoui, ta

maye gurbinsa da tsohon dan wasan Faransa Sabri Lamouchi.

Ba dai wani dalili da hukumomin kwallon kafa na kasar su ka bayar na sallamar

kocin wanda tun 2010 yake aiki da su kuma ya sami nasarar kai kungiyar

kwallon kasar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika na

shekaran nan wanda Zambia ta dauka bayan da ta doke Ivory Coast din a

bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Ana gani korar ta sa ba ta rasa nasaba da gazawar sa ta ganin kasar ta dauki

kofin na kasashen Afrika a karo na biyu a tarihin kasar.

A yanzu dai sabon kocin na Ivory Coast wanda wannan shi ne karan farko da

zai koyar a matakin koli na wasan kwallon kafa, ya na da kwanaki biyar kacal

da zai fara gwada sa'arsa a wasan da Ivory Coast za ta yi da Tanzania a gida

a rukuni na uku, wato group C na neman zuwa gasar Kofin Duniya.