Binciken cuwa cuwa: An kama kyaftin din Lazio

Stefano Mauri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kama Stefano Mauri a wani binciken sayar da wasa

'Yan sanda masu bincike a kan wani zargin sayar da wasa sun kama kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Lazio.

'Yan sanda sun ce sun tsare dan wasan na tsakiya mai shekaru talatin da biyu, Stefano Mauri, ne tare da tsohon dam wasan tsakiya na kungiyar Genoa, Omar Milanetto.

Kocin Juventus, Antonio Conte, wanda ya jagoranci kungiyar {ta Juventus} suka yi nasarar lashe Gasar Serie A, na cikin wadanda 'yan sanda ke yiwa tambayoyi.

Haka zalika 'yan sandan sun leka sansanin da 'yan tawagar Italiya zuwa Gasar cin Kofin Kasashen Turai, wato Euro 2012, ke horo, inda suka yi tambayoyi ga dan wasan baya Domenico Criscito.

A yanzu haka dai 'yan sanda na gudanar da bincike a gidaje talatin, ciki har da na 'yan wasa, da na masu horar da 'yan wasan, da ma na jami'an gudanarwa na kungiyoyin da ke buga wasa a gasannin Serie A, da Serie B, da sauran gasannin da ke kasa da su.

Wannan kame dai wani bangare ne na wani bincike da ake yi wanda tuni ya kai ga kama 'yan wasan Italiya na da da na yanzu; a watan Yunin bara ne dai Ma'aikatar Cikin Gida ta Italiya ta kafa wani kwamitin cika aiki don ya binciki zarge-zargen sayar da wasanni a kasar.

Karin bayani