Zan fice daga wasa a kan wariyar launin fata

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mario Balotelli

Dan wasan Manchester City kuma dan kasar Italiya,Mario Balotelli ya yi barazanar ficewa daga filin wasa idan aka nuna ma sa wariyar launin fata a gasar cin kofin kasashen Turai,Euro 2012, da za a fara mako mai zuwa.

Ya ce muddin aka yi min wani abu da ya danganci cin mutunci wanda ya shafi wariyar launin fata to kuwa ba abin da zan yi illa na fice daga filin wasa na kama hanyata zuwa gida.

Dan wasan ya ce ''ban amince da wariyar launin fata ba, ba zan iya jurewa ba''. Mu na shekara ta 2012 ne, abu ne da ba zai yuwu ba.

Balotelli ya kara da cewa zai kashe duk wanda ya yi gangancin jefa ma sa ayaba a titi (abin da ke nufin maida shi tamkar biri),in ya so ya tafi gidan yari.

Tsohon dan wasan na Inter Milan , dan shekara 21 yakan fuskanci matsalar wariyar launin fata akai-akai duk lokacin da ya ke buga wasa a kasar Italiya.