Frank Lampard ba zai je Euro 2012 ba.

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Frank Lampard

Frank Lampard ba zai je Gasar Euro 2012 ba saboda raunin da ya ji a cinyarsa yayin atisaye ranar Laraba.

Likitoci ne su ka tabbatar da hakan bayan da su ka kammala duba shi.

Lampard ya fara bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila ne shekaru 13 da suka wuce lokacin da ta kara da kasar Belgium, kuma a yanzu ya

gamu da wannan matsala ce da ta tilasta ma sa fita daga tawagar 'yan wasan na Ingila, kwanaki kadan kafin kasar ka kara a wasan sada zumunta

da Belgium kafin tafiya gasar cin kofin kasashen Turai.

Yanzu za a maye gurbinsa ne da dan wasan Liverpool Jordan Henderson wanda sau biyu kawai ya taba bugawa Ingila wasa, kuma sai hukumar kula

da wasan kwallon kafa ta Turai ta amince da hakan.

Gurbin na Lampard ya kara gibin da tawagar 'yan wasan na Ingila ta ke kokawa da shi a gasar bayan da Gareth Barry shi ma ya fice daga tawagar

saboda raunin da shi ma ya ji.

Wannan dai wata babbar matsala ce ga tawagar Ingilan a gasar ta Euro 2012.