Shugabannin Turai za su kauracewa Euro 2012

Euro 2012 Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kwallon Alamar 2012

Yayin da ake shirin fara gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Turai a cikin

mako mai zuwa a kasashen Ukraine da Poland ,harkar siyasa na neman yiwa

gasar kafar ungulu, inda shugabannin gwamnatocin kasashen Turan ke

barazanar kauracewa wasannin da za a yi a kasar Ukraine.

Shugabannin na neman daukar matakin ne domin nuna bacin ransu a kan

yadda gwamnatin Ukraine ke gallazawa tsohuwar fraiministar kasar Yulia

Tymoshenko.

Sai dai barazanar shugabannin kasashen na Turai da alamu ba ta yiwa

shugabanin 'yan adawa da sauran al'ummar kasar ta ukraine dadi ba inda

suke cewa, kamata ya yi su zo kasar amma su yi burus da shugaba

Yanukovych da jami'an gwamnatinsa.