An fidda Azarenka a gasar French Open

Hakkin mallakar hoto AP

Dominika Cibulkova ta fidda Victoria Azarenka wadda ita ce ta daya a fagen Tennis din mata a gasar French Open a zagaye na hudu.

Cibulkova wadda ita ce ta 15 a duniya ta doke Azarenka ne a wasan da su ka buga a ranar lahadi da maki 6-2 da 7-6.

A yanzu haka Maria Sharapova ce za ta maye gurbin Azarenka a matsayin ta daya a fagen Tennis din mata, idan ita ma ta samu kaiwa wasan karshe.

Maria Sharapova dai ce ta biyu a fagen Tennis a duniya.