Cahill ba zai buga gasar Euro ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gary Cahill ya yi karo da Joe Hart

Dan wasa bayan Ingila, Gary Cahill ba zai buga gasar Euro ba saboda kashin muka-mukinshi biyu sun goce.

Dan wasan ya samu raunin ne a wasan sada zumuncin da Ingila ta buga da Belgium a ranar Asabar, bayan ya ya yi karo na mai tsaron gida Joe Hart.

An dai kira dan wasan Liverpool, Martin Kelly ya maye gurbinsa.

Shima dai John Terry na samu rauni a cinyarsa a wasan, amma za'a kara duba lafiyarsa a ranar Talata domin ganin idan zai iya taka leda a gasar.

Kocin Ingila Roy Hodgson na fama da rashin manyan 'yan wasa saboda raunin.

'Yan wasan da su ka fice daga tawagar Ingila saboda rauni sun hada mai tsaron gida, John Ruddy da yan wasan tsakiya Gareth Barry da Frank Lampard.

Brooking ya shaidawa BBC cewa yana da kwarin gwiwa Cahill da Terry za su murmure kafin an fara gasar.