Robert Green zai bar West Ham- Gold

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Robert Green

Mai tsaron gidan West Ham, wato Robert Green zai bar kungiyar a karshen watan Yuni idan kwantaraginsa ya kare in ji David Gold daya daga cikin shugabanin kungiyar.

Kwantaragin mai tsaron gidan zai kare ne a karshen watan Yuni, kuma har yanzu bai amince ya kara wa'adin kwantaraginsa da kungiyar ba, duk da cewa an karawa kungiyar matsayi zuwa gasar Premier.

"Robert Green na zaman kansa ne a yanzu haka, kuma ya ce zai kama gabansa," In ji Gold.

"Babu wanda yake son Rob ya tafi, amma dolene mu barshi ya zabi abun da ya fi mashi alheri."

Gold dai bai ji dadin barin kungiyar da Green ya yi ba saboda a yana ganin mai tsaron gidan zai zauna a kungiyar bayan kara mata matsayin da aka yi.