Birmingham ta ba Hughton dama ya tattauna da Norwich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chris Hughton

Kungiyar Birmingham ta baiwa Norwich City dama ta tattauna da kocinta wato Chris Hughton a yayinda Norwich din ke neman sabon koci.

Kocin mai shekarun haihuwa 53 ya kai kungiyar Birmingham matakin kifa daya kwalla a gasar Championship inda Blackpool ta fidda ita.

Har wa yau ana alakanta kocin da gurbin da ake da shi a kungiyar West Brom bayan an nada Roy Hodgson a matsayin kocin Ingila.

Norwich dai a yanzu haka ba ta da koci, bayan mai horadda da kungiyar wato Paul Lambert ya koma Aston Villa.