Dirk Kuyt ya koma Fenerbahce

Hakkin mallakar hoto PA

Dirk Kuyt ya bar Liverpool inda ya koma kungiyar Fenerbahce da ke kasar Turkiyya.

Dan wasan wanda dan asalin Holland ne ya sanya hannu a kwantaragi na tsawon shekaru uku, bayan ya takawa Liverpool leda na tsawon shekaru shida.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 31 ya koma Liverpool ne daha Feyenoord a shekarar 2006, inda ya zura kwallaye 71 a wasanni 250 da ya bugawa kungiyar.

"Muna yiwa Dirk fatan alheri, kuma muna mishi godiya saboda irin gudunmuwar da ya bai wa kungiyar." In ji Liverpool a sanarwar da ta buga a shafinta.