'Alkalai za su iya tsaida wasa saboda wariyar launin fata'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michel Platini

Shugaban Hukumar kwallon kafa na Turai, Michel Platini ya ce hanya mafi a'ala ta magance wariyar launin fata a kwallon kafa shine, alkalai su rika tsaida wasa idan hakan ya faru.

A wani shirin na musamman da BBC ta yi, ta gano cewa akwai matsalar wariyar launin fata a kasashen Poland da Ukraine, wadanda kuma sune zasu karbi bakuncin gasar Euro ta shekarar 2012.

"Alkalan wasan za su iya tsayar da wasan, suna da hurumin yin haka saboda wariyar launin fata." In ji Plantini a hirar da ya yi da BBC.

"Ina ganin wannan ne hanya mafi a'ala na magance wariyar launin fata a harkar kwallon kafa."

Platini ya yi watsi da zargi da maganar da ake yi na cewa martabarsa za ta zube idan an samu matsalar wariyar launin fata a gasar Euro.

Platini ya dai nace cewa alkalan wasa za su nunawa duk wani dan wasa katin gargadi idan ya fita daga filin wasa saboda an yi mishi zagin wariyar launin fata.

Dan wasan Italiya da kungiyar Manchester City, wato Mario Balotelli ya yi barazanar ficewa daga filin wasa, muddin an yi mishi kalamun wariyar launin fata.