'Ina so in yi murabus daga taka leda a Madrid'- Ronaldo

Hakkin mallakar hoto AFP

Cristiano Ronaldo ya ce yana so ya yi murabus daga harkar tamoula a Real Madrid bayan ya lashe kofin laliga da kungiyar a karon farko a kungiyar.

Dan wasan wanda Madrid ta siya daga Manchester United a kan fam miliyan 80 ya zura kwallaye 46 a kakar wasan da aka kammala a gasar laliga.

"Idan ta nine ina so in ci gaba da zama a Real Madrid har sai lokacin da zan yi murabus a harkar kwallon kafa." In ji Ronaldo.

"Zan iya sa hannu a kwantaragi na tsawon shekaru goma a yanzu haka, amma sai yadda ta yi wu."