Afrika ta kudu ta sallami kocinta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pitso Mosimane

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudu ta sallami kocin tawagar kwallon kafan kasar na Bafana-Bafana wato Pitso Mosimane daga aiki.

Sallaman kocin ya biyo bayan kunnen dokin da kasar ta buga da Habasha a gida a ranar Lahadin da ta gabata a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya.

Steve Komphela, daya daga cikin mataimakan kocin ne zai maye gurbinsa a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da kasar za ta buga da Botswana a ranar asabar.

Hukumar kwallon kasar wato Safa ta ce ta dau matakin ne domin dawo da martabar kwallon kafa a kasar.

Duk da matsalolin da tawagar kasar ke fuskanta, Shugaban Hukumar kwallon kafan kasar, Kirsten Nemantandani ya jinjinawa Mosimane saboda irin gudunmuwar da ya bada.