Gasar Euro: Keane ya yabawa hadin kan yan wasan Ireland.

Gasar Euro: Keane ya yabawa hadin kan yan wasan Ireland.

Kyaftin din Ireland Robbie Keane yayi ammanar cewa hadin kan dake tsakanin yan wasan Ireland zai karfafa duk wani tasirin da zasu yi a gasar EURO.

Duk da cewa Kevin Foley ya bar wurin da 'yan wasan ke horo a makon da ya gabata amma Keane yace ba za'a sami wani batu da zai kawo ce-ce-ku ce a wanan gasa ba.

Shekaru goma da suka wuce , Roy Keane ya bar yan wasan kwallon kafa na Ireland a ranar jajibirin gasar kofin duniya ta shekerar 2002.

' Irin 'yan wasan da mu ke dasu , da kuma yada suka fahimci juna wani abu ne me kyau" a cewar kyaftin din.

Yankin Ireland na ci gaba da shirye shirye game da gasar kuma a daren yau za su yi karawa ta karshe tsakaninsu da Hungary a Budapest a wasan sada zumunci.