Kagawa zai koma Manchester United

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shinji Kagawa

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sa hannu a kan yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya na kasar Japan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borusia Dortmund ta kasar Jamus akan kudi fam miliyan goma sha biyu.

Dan wasan me shekaru 23 za'a yi masa gwaje- gwajen lafiyarsa kuma zai bukaci izinin aiki a Birtaniya, sai dai Manchester tana sa ran cewa za'a kamala komai a karshen watan da muke ciki.

Kagawa ya zira kwallaye 13 a wasanin 31 na Budesliga yayinda kungiyar Dortmund ta yi nasarar daukar kofi a kakar wasani bana.

Dan wasan wanda ya yanzu ke yiwa kasarsa hidima, ya buga kwallo a karawar da Japan tayi da Oman inda ta lallasa Oman din da ci uku ba ko daya, a wasan neman cancantar shiga cikin gasar copin duniya ta FIFA.

Ana sa ran isowar Kagawa za ta sa magoya bayan Manchester 'yan Asiya su ji da di, sai dai ba bu tabbas akan ko dan wasan tsakiya na kasar Koriya ta Kudu Park Ji Sung zai cigaba da taka leda a kungiyar ta Manchester.