Ingila ba ta tsoron Faransa- Stewart Downing

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stewart Downing

Dan wasan Ingila, Stewart Downing ya ce tawagar Ingila ba ta tsoron haduwarta da Faransa a ranar Litinin a gasar Euro.

Tawagar Ingila, wadda Roy Hodgson yake jagoranciza ta hadu ne da Faransa a wasanta na farko a gasar, sannan kuma ta kara da Sweden a ranar 15 da watan Yuni, kafin kuma Ukraine bayan kwanaki hudu.

Downing, mai shekarun haihuwa 27, ya ce: "Muna da kwarin gwiwa zamu samu sakamakon da muke nema a wasan. Ba ma jin tsoron su.

"Tawagarmu tana da kwarewa.. Mun san inda su ka kware kuma mun san inda suke lakwa-lakwa."

Dan wasan ya musanta cewa 'yan wasan kasar na korafi a kan cewar ba'a sanya sunan Ferdinand ba a tawagar Ingila, inda ya ce kocin kasar na da hurumin zabar duk dan wasan da ya ke so.