Ashley Cole ya yi atiseye da sauran takwarorinsa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ashley Cole

Ashley Cole ya yi atiseye da sauran yan wasan kwallon kafa na Ingila a filin wasa na Hutnik dake Krakow yayinda kasar ke ci gaba da shirye -shiryen gasar turai ta bana.

Cole be halarci liyafar da aka shiryawa yan wasan Ingila a Krakow ba da yammacin alhamis saboda yana fama da ciwon ciki.

Sai dai dan' wasan baya dake taka leda a klub din Chelsea, me shekaru 31 ya kasance cikin yan wasan farko da su ka yi atiseye a gaban magoya bayansu dubu uku.

Jermain Defoe shi ka dai ne dan wasan da be halarci atiseyen ba saboda rasuwar mahaifinsa, abin da kuma ya sa ya koma gida Ingila.

Ingila za ta share fage a wasan da zasu yi da Faransa a birnin Donetsk a ranar litinin me zuwa a gasar turai ta bana