An nuna wariyar launin fata ga ya wasan Netherlands

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yan wasan Netherlands

Hukumar kwallon kafa ta turai watau UEFA ta tabbatar da cewa wasu sun ringa rera wakokin wariyar launin fata ga yan wasan kwallon kafa ta kasar Netherlands a lokacin da suke astiseye.

Sai dai hukumar ba ta ce ko za ta binciki lamarin ba, wanda ya faru a Krakow ,a kasar Poland.

Kyaftin din Netherlands Mark Van Bommel ya ce an ringa rera wakokin biri ga abokanen wasansa.

" Idan aka sake samun aukuwar lamari irin haka a inda yan wasa ke astiseye, UEFA za ta yi nazari akan matakan da zata dauka domin samar da kariya ga yan wasa"

Hukumar ta UEFA ta ce hukumar kwallon kafa ta Netherlands ba ta gabatar mata da koke ba sai dai wani jami'i a hukumar kwallon kafa na Netherlands ya shaidawa BBC cewa ba za su shigar da koke ba .

Ko da yake Van Bommel ya yi korafi ne akan matsalar wariyar launin fata, amma hukumar kwallon kafa ta Netherlands ta ce an kuma rera wakokin nuna adawa da gasar saboda garin ma Krakow ba ya cikin wuraren da kasashe za su yi wasa.