Chelsea na shirin nada Di Matteo

Hakkin mallakar hoto PA

Chelsea na shirin tabbatar da nadin Roberto Di Matteo a matsayin kocin kungiyar a wannan makon da muke ciki.

Wakilin kocin sun tattauna da jami'an Chelsea a karshen mako, kungiyar ta tabbatar masu cewa za'a nada kocin a matsayin mai horadda 'yan wasan kungiyar na dindin.

Di Matteo ya amince zai karfi mukamin amma zai a makon da za'a shiga ne za'a cimma yarjejeniya game da kwantaragin da za'a baiwa kocin.

An dai nada Di Matteo a matsayin kocin Chelsea na wucin gadi ne bayan sallaman Andre Villas-Boas a watan Maris.