Jamus za ta taka rawar gani nan gaba- Loew

Hakkin mallakar hoto AFP

Kocin Jamus, Joachim Loew ya ce tawagarsa za ta taka rawar gani sosai nan gaba, bayan nasarar farko da kungiyar ta samu a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro.

Dan wasan Bayern Munich, Mario Gomez ne ya zura kwallo daya tilo da ya ba Jamus nasara a wasan da ta buga da Portugal a rukunin B.

"Gomez kwararren dan wasa ne, dama daya ya samu kuma ya zura kwallon." In ji Loew.

"Abun da ya fi mahimmacin shine nasara. Gasar cin kofin Turai, kamar gasar Formula ce, tsere daya ne ba'a shiryawa"

Jamus dai ta fuskanci kalaubalen zura kwallo a wasan saboda sai ana minti 72 uku ne Gomez ya samu ya zura kwallo a ragar Portugal.

Jamus za ta buga a wasanta na biyu ne da kasar Denmark a ranar 13 ga watan Yuni.