Petrov zai ci gaba da zama kyaftin din villa

Hakkin mallakar hoto AFP

Kocin Aston Villa Paul Lambert ya ce Stiliyan Petrov zai ci gaba da zama kyaftin din kungiyar duk da cewa dai yana kokarin nada wani sabon kyaftin a kungiyar.

Petrov na karbar maganin saboda cutar rashin isasshen jini da ya samu a watan Mayu.

"Stiliyan har yanzu shine kyaftin din kungiyar babu tantama." In ji Lambert.

"Zai taimakawa kungiyar saboda yana da mahimmaci. Amma ina bukatar wani kyaftin din."

Lambert, ya yi da Petrov a lokacin suna Celtic tare, kuma ya ziyarci tsohon abokin nasa domin kai masa gaisuwa a lokacin da ya kamu da cutar.