Ingila ta buga kunnen-doki da Faransa

Hakkin mallakar hoto AP

Joleon Lescott ya zura kwallonsa ta farko wa Ingila a wasan da kasar ta buga da Faransa a gasar cin kofin Nahiyar Turai, amma dan wasan Faransa Samir Nasri ya fanshe kwallon, abun da kuma hanawa Ingila nasara.

Dan wasan Ingila Lescott ya sanya Ingila a gaba ne da kaa bayan da Steven Gerrand ya cillo kwallon daga dama a bugun falan daya.

Amma ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne abokin wasan Lescost a kungiyar Manchester City wato Samir Nasri ya fanshe kwallon bayan ya harbo ta daga yaddi 20.

Alou Diarra ya so ya kara wata kwallo a ragar Ingila amma sai Joe Hart ya tare kwallon, shima dai James Milner ya samu dama amma sai ya buga ta a gefen raga.

France dai tafi Ingila samun dama a wasan.

Ingila dai za ta buga wasanta na gaba ne da Sweden a ranar Juma'a a yayinda kuma Faransa za ta hadu da daya daga cikin masu daukar nauyin gasar wato Ukraine.