Ireland ba ta yanke-kauna ba

Kocin Ireland Giovanni Trapattoni Hakkin mallakar hoto inpho
Image caption Kocin Ireland Giovanni Trapattoni

Mai horar da 'yan wasan kasar Ireland, Giovanni Trapattoni ya ce kungiyarsa ba ta yanke-kaunar kai labari a gasar cin Kofin nahiyar Turai ba.

Yayi wannan furucin ne duk kuwa da kayen kasar ta sha na ci uku da daya a hannun kasar Crotia.

Kasar Crotia ta lallasa Ireland ne a jiya Lahadi, kayen da ya sa Ireland ta zama ta baya a wani rukuninta, wanda kuma ake yi wa kallon mai wuyar gaske.

A ranar Alhamis mai zuwa ne kasar Ireland za ta kara da kasar Spain, kafin su fuskanci kasar Italiya a ranar goma sha takwas ga watan Yuni.

Shi ma dan wasan gaba na Kungiyar kwallon kafa ta kasar Ireland, Kevin Kilbane ya yi amanna da cewa kungiyarsa za ta kai labari a gasar.

Ya shaida wa BBC cewa "ci uku da aka yi mana ba karamin koma-baya ba ne, amma mun saba da tabuka abin kirki a lokutan da muka samu kanmu a halin tsaka-mai-wuya."

Kasar Spain ta yi kare-jini-Biri-jini da takwararta ta Italiya a wasan da suka yi ranar Lahadin da ta gabata.

Kuma akwai yiwuwar sai kasar Ireland ta samu nasarar a kan kungiyoyin biyu kafin ta kai zagaye na gaba.