Nadal ya lashe gasar French Open a karo na bakwai

Hakkin mallakar hoto AFP

Rafael Nadal ya kafa tarihi, inda ya lashe gasar French Open a karo na bakwai a jere, bayan ya doke Novak Djokovic a wasan karshe da aka kammala a ranar Litinin.

Nadal ya lashe wasanni ne na maki 6-4 6-3 2-6 7-5.

An fara wasan karshen ne a ranar Lahadi amma saboda ruwan sama aka dakatar da wasan a yayinda aka kammala a ranar Litinin.

Kafin a dakatar da wasan dai, Rafeal Nadal ne ke kan gaba da wasanni biyu a yayinda Djokovic na da wasa daya wato 6-4 6-3 da kuma 2-6.

A yanzu haka dai Rafeal Nadal ya lashe kyautar Grand Slam 11 a tarihinsa.

'Yan wasa uku ne kawai ke gaban Nadal a cikin wadanda su ka lashe kyautar ta Grand Slam, kuma 'yan wasan su ne Roger Federer wanda ya lashe kyautuka 16, Pete Sampras kyautuka 14 da kuma Roy Emerson mai kyautuka 12.