Uefa za ta binciki zargin wariyar launin fata

Hakkin mallakar hoto Reuters

Uefa za ta binciki zargi zagin wariyar launin fata da 'yan kallo su ka yi a gasar cin kofin nahiyar Turai a wasan Spain da Italiya da kuma Rasha da Jamhuriyar Czech.

Wata kungiyar magoya bayan Spain, ta ce wasu daga cikin 'ya 'yanta sun yiwa dan wasan Manchester City da kuma Italiya, Mario Balotelli zagin wariyar launin fata.

Shima dai dan wasan Jamhuriyar Czech, Theodor Gebre Selassie ya shaidawa manema labarai cewa ya lurra cewa ana mishi zagin wariyar launin fata a wasan da kasar shi ta buga da Rasha.

Uefa dai ta ce har yanzu ba ta daukin mataki game da al'amarin.

Wata sanarwa da Uefa ta fitar ta ce: "Bayan mun samu wasu bayanai daga kafofi masu zaman kansu a kan zargin wariyar launin fata a wasan Spain da Italiya da kuma Rasha da Jamhuriyar Czech, Uefa a yanzu haka ta fara bincike."

Kasar Jamhuriyar Czech da kuma Italiya dai ba su gabatar da korafi a kan batun ga Hukumar Uefa ba.