Arsenal na dab da siyan Giroud

Hakkin mallakar hoto AFP

Arsenal ta kusan kammala cimma yarjejeniyar siyan dan wasan Montpellier da Faransa Olivier Giround a kan Fam miliyan 12.

Kungiyar dai za ta tabbatar da siyan dan wasan mai shekarun haihuwa 25 a cikin makon da muke ciki.

Kocin kungiyar, Arsene Wenger na niyyar amfani da dan wasan tare da sabon dan wasan da ya siya Lukas Podolski da kuma Robin van Persie duk a gaba.

Dan wasan dai na cikin tawagar Faransa da ke gasar cin kofin nahiyar Turai, amma dai bai buga wasan farko da kasar ta buga da Ingila.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 21 a kungiyarsa a gasar Ligue 1 ta Faransa a kakar wasan bara.