Chelsea ta nada Di Matteo a matsayin koci na din-din-din

Hakkin mallakar hoto PA

Kungiyar Chelsea ta nada Roberto Di Matteo a matsayin koci na din-din-din na tsawon shekaru biyu.

Wakilan kocin dai sun debe karshen mako ne su na tattaunawa da jami'an kungiyar wadanda kuma su ka basu tabbacin cewa kocin ne ke kan gaba cikin wadanda mai kungiyar wato Roman Abramovich ke so ya nada.

Di Matteo, mai shekarun haihuwa 41, ne aka nada a matsayin kocin wucin gadi a lokacin da aka sallami Andre Villas-Boas a watan Maris.

Tun da kocin ya jagoranci kungiyar an doke ta na a wasanni uku cikin 21 da ta buga.

Har wa yau shine ya jagoranci kungiyar inda ta lashe kofin gasar zakarun Turai da kuma gasar cin kofin FA.