Ingila ba ta da karfi idan babu Rooney- Hodgson

Kocin Ingila Roy Hodgson ya amince cewa tawagar kasar na fuskantar kalubale saboda rashin Wayne Rooney, wanda ya bayyana a matsayin 'kwarraren dan kwallo'.

An dai dakatar da dan wasan ne daga taka leda a wasanni biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai, abun da kuma zai sa ba zai samu buga wasan da kasar za ta buga ba a ranar Juma'a da Sweden.

"A gaskiya babu tantama muna jin rashinsa sosai." In ji Hodgson.

"Kwararren dan wasa ne a duniya, kuma idan yana taka mana leda zamu fi karfi."