Swansea na shirin nada Laudrup a matsayin koci

Hakkin mallakar hoto Getty

Swansea City na shirin bayyana sunann Michael Laudrup a matsayin sabon kocinta.

BBC ta samu bayanan da ke nuni da cewa, kungiyar za ta gabatarda kocin ne a karshen mako.

Micheal Laudrup dai ya taba takawa Real Madrid da Barcelona da kuma kasar Denmark leda, kuma zai maye gurbin Brendan Rodgers ne wanda ya koma Liverpool.

Swansea dai ta kammala kakar wasa bana ne a matsayin ta 11 a tebur a karonta na farko a gasar Premier.