An ci tarar Croatia saboda zagin Balotelli

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kula da kwallon Turai, wato Uefa ta ci tarar Croatia Euro dubu 80 saboda magoya bayan kasar sun yiwa dan wasan Italy wato Mario Balotelli zagin wariyar launin fata.

Har wa yau, hukuncin ya hada da laifin jefa a abubuwa a filin wasa da magoya bayan kungiyar su ka yi a ranar alhamis din da ta gabata.

Akwai dai mai daukar hoton da ya ce ya ga wani jami'in kula da filin wasa na daukar ayaban da aka jefo cikin fili a yayinda magoya bayan Croatia ke zagin Maro Balotelli a yayinda su ke kiransa biri.

Croatia na da kwanaki uku na daukaka kara game da hukuncin da Uefa ta dauka a kanta.

Tun da farkon gasar ne dai Uefa ta ci tarar Croatia fam dubu 20 da dari biyu bayan magoa bayanta sun yi jifa cikin filin wasan, a wasan da kasar ta buga da Jamhuriyar Ireland.