Jamus za ta fuskanci hukunci na biyu daga Uefa

Hakkin mallakar hoto UEFA

Uefa ta fara shirye-shiryen ladabtar da Hukumar kwallon kafan Jamus saboda rashin da'ar da magoya bayan kasar su ka nuna a wasan da ta doke Denmark da ci biyu da daya.

An dai tuhumi Jamus ne saboda magoya bayanta sun yi wasa da abubuwan fashewa da kuma daga allunan masu rubutun da bai da ce da da kuma rera wakoki da basu da ce ba a lokacin wasan.

Wasu masu sa ido a harkar wariyar launin fata sun ce sun ga wasu rubuce rubuce da basu dace ba a bangaren Magoya bayan Jamus.

A ranar asabar ne dai Uefa za ta yanke hukunci game da lamarin.

Uefa dai ta ci tarar Jamus fam dubu goma saboda rashin da'ar da magoya bayan kasar su ka nuna a wasan da kasar ta doke Portugal da ci daya mai ban haushi.