Drogba ya koma kungiyar Shanghai Shenhua

Hakkin mallakar hoto PA

Tsohon dan wasan Chelsea, Didier Drogba ya rataba hannu a kwantaragi na tsawon shekaru biyu da rabi domin takawa kungiyar Shanghai Shenhua da ke kasar China.

Zai hadu ne da tsawon abokin wasansa a Chelsea wato Nicolas Anelka.

Drogba, mai shekarun haihuwa 34, ya ce: "Duk na duba kungiyoyin da ke nema in taka masu leda amma ina ganin kungiyar Shanghai Shenhua ce tafi da cewa a yanzu haka."

Dan wasan ya takawa Chelsea leda ne na karshe , inda ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da Chelsea ta yi nasara a kan Bayern Munich.

Wasan farko da Drogba zai bugawa kungiyar shine wanda za ta hadu da Manchester United a ranar 25 ga watan Yuli a wasanni share fagen fara kakar wasa da Manchester United za ta yi a China.

Kofin Premier Ukku

Drogba ya fara takawa Chelsea leda ne bayan da ya baro Marseille akan pan million 24 a shekarar 2004.

Shi ne daya daga cikin yan wasa na farko farko da Jose Mourinho ya fara siyowa.

Ya taimakawa kulob din Chelsea nasarar daga kofin Premier har sau ukku, da kofin FA sau hudu da kofin lig-lig guda biyu a shekaru takwas da ya yi ya na yi wa kulob din wasa.

A wannan lokaci ya samu daukaka zuwa na hudu a tarihin maciya kwallon Chelsea, inda ya zura kwallaye 157.

Drogba ya ce, "ina fatan fuskantar sabon kalubale da basira kan sabuwar alada, kuma ina farin ciki da cigaban wasan lig na kwallon kafar China."

Drogba a Shanghai Shenhua

Shanghai Shenhua ne kulob na farko da ya fara cin gashin kan sa daga mallakar gwamnatin China, kuma dan kasuwar nan Zhu Jun shi ne ya mallaki mafi akasarin hannun jarin kulob din.

A baya kulob din ya sai sanannun yan wasa kamar Carsten Jancker da Jorg Albertz.

Su na wasansu ne a filin wasan na Hongkou, wanda ke daukar yan kallo dubu talatin da biyar.

Zhu Jun ya yi amannar cewa shigar Drogba kulob din a watan Yuli zai taimaka mata wurin karfafa kwallon kafar kulob din.