Drogba ya koma kungiyar Shanghai Shenhua

Hakkin mallakar hoto PA

Tsohon dan wasan Chelsea, Didier Drogba ya rataba hannu a kwantaragi na tsawon shekaru biyu da rabi domin takawa kungiyar Shanghai Shenhua da ke kasar China.

Zai hadu ne da tsawon abokin wasansa a Chelsea wato Nicolas Anelka.

Drogba, mai shekarun haihuwa 34, ya ce: "Duk na duba kungiyoyin da ke nema in taka masu leda amma ina ganin kungiyar Shanghai Shenhua ce tafi da cewa a yanzu haka."

Dan wasan ya takawa Chelsea leda ne na karshe , inda ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da Chelsea ta yi nasara a kan Bayern Munich.

Wasan farko da Drogba zai bugawa kungiyar shine wanda za ta hadu da Manchester United a ranar 25 ga watan Yuli a wasanni share fagen fara kakar wasa da Manchester United za ta yi a China.