Mido ya koma kungiyar Barnsley

Hakkin mallakar hoto empics

Barnsley ta sayi tsohon dan wasan Tottenham da Middlesbrough Mido.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 29 dan asalin kasar Masar ne kuma ya cimma yajejeniyar takawa Barnsley leda na tsawon shekaru biyu.

Kocin kungiyar Keith Hill ya shaidawa shafin kungiyar cewa; " A shirye nake inyi aiki tare da kwarrarren dan wasa."

Mido, wanda ya takawa kungiyar Wigan da West Ham leda, an sallame shi ne daga kungiyarshi ta Zamalek a watan Mayu saboda rashin jituwa tsakaninsa da kocinsa Hassan Shehata.