Alonso ya lashe gasar Valencia Grand Prix

Hakkin mallakar hoto Reuters

Direban Ferrari Fernando Alonso ya zama na farko da ya lashe tsere biyu a bana, bayan da ya yi nasara a gasar tseren motoci ta Valencia Grand Prix.

Alonso ya fara ne a matsayi na 11 a tseren sannan ya koma a matsayi na hudu bayan da Lewis Hamilton da Romain Grosjean su ka tsaya a duba lafiyar motarsu.

Shi kuwa Sebastian Vettel ya fita ne daga tseren bayan motarsa ta samu matsala.

Daga baya ne kuma Alonso ya sha gaban sauran inda ya kammala tseren a matsayi na daya.

Direban Lotus Kimi Raikkonen ne ya zo na biyu sannan kuma direban marsandi, wato tsohon zakaran tseren motoci, Micheal Schumacher ya kare a matsayin na uku, wanda shine karo na farko da ya samu wannan matsayin tun bayan da ya dawo tsere a shekarar 2010.